Kamfanin jiragen sama na Air Peace a Najeriya, ya bayyana shirinsa na kwaso ƴan Nijeriya da suka makale a Sudan, Arewa maso Gabashin Afirka kyauta idan har gwamnatin tarayya za ta samar masa da filin sauka da tashin jirgin sama mai aminci da tsaro a kasashen da ke makwabtaka da Sudan.
Shugaban kamfanin, Allen Onyema ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a yau Litinin.
A cewarsa, daliban Najeriya da sauran wadanda su ka makale a kasar da ta faɗa yaƙi kwanan nan na bukatar agajin gaggawa.
Onyema ya ce ya zama dole ya taimaka domin kwaso ƴan Nijeriya da su ka makale a kasar da ake gabza yaki, duba da cewa bai kamata Nijeriya ta bari a kashe mata ko mutum daya a Sudan ba.
“Haka kuma, Air Peace a shirye ya ke ya kwashe yan Nijeriya da suka makale a Sudan kyauta idan gwamnati za ta iya kai su filin jirgin sama mai aminci da tsaro a duk kasashen da ke makwabtaka da Sudan. Bai kamata a bar komai a hannun gwamnati kadai ba.
“A shirye muke mu yi cikin gaggawa. Babu bata lokaci. Duk wani aiki da zai inganta martabar kasa, hadin kan kasa, zaman lafiya da hadin kai, to mu ne a ciki
“Har ila yau, ba gudu ba ja da baya wajen so da yarda da ƙasar mu Nijeriya. Mu na jira a kai ƴan Nijeriyar da ke Sudan zuwa Kenya ko Uganda ko wata ƙasa, mu kuma za mu je da gaggawa mu kwaso su. Yanzu haka har iyayen wasu ɗaliban sun fara kira gare mu da mu taimaka. A shirye muke mu sake yin haka,” inji shi.