Yaki Ne Wanda Ba A San Labarinsa Sosai Ba. Wanda Aka Yi Shi Akan Ikon Mallakar Wasu Tsibirai A Tafkin Chadi. Yakin Ya Fara Ne A Lokacin Da Wata Runduna Karkashin Jagorancin Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Kasar Chadi' Idriss Déby Ta Mamaye, Wasu Sassan Jihar Borno Ta Najeriya, A Lokacin Mulkin Hissène Habré Na Kasar Chad 🇹🇩 Wanda Yazo Dai-Dai Da Zamanin, Mulkin Farar Hula Ta' Marigayi Alhaji Shehu Aliyu Shagari.
Yakin Ya Faru Ne A Lokacin Yakin Tsakanin Kasar Chad Da Libya. Kuma Jim Kadan Kasar Chadi Ta Fuskanci Yakin Basasa, In Da Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Na Najeriya Suka Tsinci Kansu Cikin Fada. Wani Abin da Ya Kara Dagula Dangantakar Chadi Da Najeriya Shi Ne Rikicin Yankuna A Kusa Da Tafkin Chadi, Wanda Ya Dade Yana Haifar Da Rikici.
A Ranar 18 Ga Afrilu, 1983, Sojojin Saman Kasar Chadi Suka Mamaye, Tsibirai 19 Na Najeriya A Yankin Tafkin Chadi. Bada Wani Bata Lokaci Ba Jiragen Yakin Najeriya Kirar Mig 21 Suka Soma Luguden Wuta Akan Sojojin Kasar Chadi.
Sojojin Najeriya sun yi nasarar kwato tsibiran, sannan kuma sun fatattaki 'yan kasar Chadin mai nisan kilomita 50 daga kan iyakokin kasar.
A Gefe Guda Muhammadu Buhari. Shugaban Kasar Nijeriya Na Yanzu. Yana Babban Jami'in Kwamandan (GOC) Na Runduna Ta Uku Ta Jos. Ba Tare Da Ya Jira Umarni Daga Gwamnatin Tarayya Ba. Ya Debi Sojoji Suka Rararaka Sojojin Chadi Har Cikin Kasar Su. Saida Sojoji Najeriya Suka Shiga Kilomita 50 A Cikin Kasar Chadi Kuma Ya Datse Boda Ba shiga Ba Fita, Har Saida Kasar Chadi Ta Kai Karar Najeriya Majalisar Dinkin Duniya. A Kan Kutsen da Sojojin Najeriya A Karkashin Muhammad Buhari Su Kayi Mata.
Bada Wani Bata Lokaci Ba Shugaban Kasar Najeriya Shehu Shagari Ya Baiwa Buhari Umarni Ya Fita Daga Cikin Yankin Kasar Chad, Aikin Da Dama Ba'a Sashiba Amma Buhari Yayi kemagadas Yaki Bin Umarni.
A Lokacin Majalisar Dattijan Najeriya Ta Kafa Kwamitin Binkice A Karkashin Sanata Sabo Aliyu Bakin Zuwo, A Kan Lamarin. In da Majalisa Ta Kirawo Muhammadu Buhari Domin Jin Ba'asi.
Muhammadu Buhari Ya Baiyana A Gaban Majalisar, Dauke Da Hular Soja A Kansa, Nan Da Nan Sanata Sabo Bakin Zuwo,Ya fusata ya Harare Shi Tare Da Daka Masa Tsawa" Yace Kai Cire Hular Nan, Nan A Gaban Manyan Najeriya Kake Ba Barikin Soja Ba.
Yakin yana daya daga cikin musabbabin juyin mulkin da Najeriya ta yi a shekarar 1983. Saboda Nuna gazawar shugaba Shagari da jami’an sa suka yi, wanda hakan ne ya sa Buhari ya fito fili ya yi watsi da umarnin da aka ba shi, ya nuna yadda ake takun saka tsakanin sojoji da gwamnatin farar hula. A ranar 31 ga Disamba, 1983, Muhammadu Buhari ya karbi mulki a Najeriya, inda ya kawo karshen Jamhuriyar Najeriya ta biyu