Gwamnatin Iran: Sayyid Ali Khamne'i Ya Bukaci Sojin Kasar Tasa da su Shirya Tsaf Da Kuma kula sosai Akan Makiya Duk Wani Motsin Makiya.
Shugaban Gwamnatin Musulinci a Iran, Sheikh Khamene'i Aliy, ya tabbatar da cewa kasar Amerika na da wasu muradai a kasar Iraki da Afganistan, to amma babban burinsu na karshe ita ce kasar ta jamhuriyar musulunci Iran ka dai.
To amma dai har yanzu ta kasa saboda tsayin daka da jajircewa na al’ummar kasar bisa riko da manufofin juyun juya halin musulinci da kuma juriya.
Khmanei yayi wannan jawabin ne yau Lahadi, a lokacin da yake ganawa da wasu daga cikin kwamandoji da manyan jami'an sojojin kasar ta Iran.
Ta wani fannin kuma jagoran ya bukaci sojin kasar dasu mai da hankali sosai a kan duk wani tsarin da makiya sukeyi ta hanyar saka ido na matsakaici da na dogon lokaci.