Gwamnatin​ Iran Ta Fara Aikin Kera Sabin Makamai Masu Linzaami Wadanda Za su Iya Kakkabo Tauraron Dan'adam A Sararin Sama.

Gwamnatin​ Iran Ta Fara Aikin Kera Sabin Makamai Masu Linzaami Wadanda Za su Iya Kakkabo Tauraron Dan'adam A Sararin Sama.


Shugaban dakarun kare juyin juya halin musulunci a Iran General Hussain Salami ya bada sanarwar cewa masana a cikin dakarun (IRGC) suna cikin aikin kera makamai masu linnzami wadanda suke sauri fiye da sauti, wadanda kuma za'ayi amfani da su domin kakkaboo taurarin dan'adam dake sararin sama.


Babban gidan talabijin na Presstv a Tehran ya fitar da gen Salami yana fadar haka a jiya asabar a Tehran, ya kuma kara da cewa na'urori da kuma wadannan makamai suna da karfin hana kutsen tauraron dan'adam na makiya a kan sararin samaniyar Iran, sannan suna iya tare duk wani tauraron dan’adam wanda yake da Rada a duk fadain Duniya.


General Salami ya kammala jawabin sa da cewa makamin yana da karfin inganci ta yada zai iya samun duk wani abu mai tafi a cikin ruwa, kuma yana iya tuka jirgin ruwa a duk inda ake so ba tare da matuka da ma'aikatan jirgin sun samu matsala ba.

Previous Post Next Post