Kotu Ta Aike Da Aminin Miji Gidan Yari Sakamakon Lallashin Matarsa.

Shari'a

 
Kotun shari'ar addinin musulinci dake zamanta a unguwar Kwana Huɗu Kano, ta aike da wani mutum zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya bisa , tuhumar Lallashin matar Aure tare da bayar da bayanan gaibu.

Laifin da ake zargin, Murtala Abdulmuminu da aikata wa ya saɓa da sashi na 389 da 336 na kundin SPCL.

Tunda fari wani amininsa ne mai suna Isyaku Sulaiman , ya ke tuhumarsa da cewa bayan sun samu saɓani da matarsa , shi kuma ya ci gaba da zuwa wajen ta, tare da yi mata Kyaututtuka da dai sauransu a gidanta na Aure, kuma tare da shi aka nemo aurenta.

Hakan ce ta sanya, suka fara samun saɓani da mijinta har ta kai tabar gidan mijin , sannan kuma wanda ake zargin ya yi ikirarin zai kashe shi.

Mai gabatar da ƙara Aliyu Abidin Murtala ya karanto masa ƙunshin tuhumar da ake yi masa , inda ya musanta zargin.

Mai gabatar da ƙarar ya ce za su gabatar da shaidundu a gaban kotun.

Sai dai lauyan dake kare wanda ake tuhuma ya roƙi kotun ta bada belin sa , sai dai Alƙalin kotun mai shari'a Mallam Nura Yusuf Ahmad ya sanya ranar 15 ga watan Mayu 2023 dan ci gaba da sauraran shari'ar .

ATP Hausa TV
Previous Post Next Post