MACE A MAHANGAR ZAMANTAKEWA !

A mafiya rinjayen tunanin mutanenmu ( hausawa) suna daukar mace a mahangar zamantakewa wata abace ta biyan bukata kadai, ba tare da duban tarin damarmakin da Allah ya bata ba.
Meyasa bama cire sha'awan da ke tsakaninmu ( mace da namiji) mu dora ita macen a mahangar zamantakewa da rayuwa na yau da kullum?. 

A cikin irin al'ummar da muke da su a kasata (Nigeria) hausawa na cikin kaso mafi rinjaye da suka mayar da mace kayan anfani da biyan bukata, bayan wannan mace batada wani anfani a wajensu, kadan daga cikin su ne ke zama da mace a matsayin abokiyar rayuwa. 

Shin ko kinsan cewa kece mutum na farko daya bayar da dama dari bisa dari na wanzar da wannan mummunan tunanin a tsakankanin al'umma ? .

Tun farko ke ce kike daukar kanki a matsayin wata abar sha'awa, birgewa da daukan hankali ga namiji, kika dauka banda biyawa miji bukatar sha'awarsa da yi masa sauran ayyukan gida baki da wani sauran anfani, taya shi kuma bazaya daukeki a yanda kike so a daukeki ba. Tabbas ke abar burgewa da sha'awa ce, Amma idan wannan burgewa din da sha'awan suka kare shikenan kin gama aiki kenan? Ansar itace A'a kuma eh ga wacce ta zabi hakan. Kinada damar kasancewa abokiyar zamantakewa ga mijinki ta hanyoyi da yawan gaske ba sai iya wa'yancan ba.  

Mace a mahangar zamantakewa ana bukatar ta zamana ko da so da kauna ya kare a tsakanin ta da mijinta to still akwai dalilin da zaya zaunar da ita gareshi , bawai ina nufin tunda ta haifi yara yanzu zamansu zatayi ba, a'a ko basu haifi kowa ba har suka shekara dari to dalilan kasancewarsu tare kullum suna nan. Ba its girki, haihuwa, raino, kwanciya kadai kike da tasiri ba. 

Anaso ne ki kasance a matsayin masoyiya, matar aure, abokiyar rayuwa, abokiyarsa, abokiyar sirrinsa, abokiyar shawararsa, abokiyar nemansa, abokiyar rufin asirinsa, abokiyar karatunsa, abokiyar namen aljannarsa, abokiyar kare mutuncinsa, abokiyar, abokiyar, abokiyar....

Kowane daya daga cikin wa'yannan abubuwan, ya zama idan kun rabu anan to zaku hadu acan, idan soyayyah ta kare to zaku cigaba da zama a matsayin abokai, idan abota ta kare zaku cigaba da zama a matsayin abokan rufin asiri, kowane daya ya kauce to ya zamana kunada wanda zaku tsaya akai. Bawai ki zamana kina tsufa kika fara gazawa da biya masa bukata da aikace-aikacen gida shikenan kin tashi aiki ba. A'a duk tsawon tafiya aje dake. Kece kike bada damar kasancewarki mace a mahangar zamantakewa ko kuma mace a matsayin abun biyan bukata, motsinki da aikinki su ne suke fassara hakan.

Amma yanada kyau ki gane cewan ba dan wannan kadai Allah yayo ki ba, kuma yanda Allah zaya tambayi namiji akan yanda ya gudanar da rayuwarsa, kema haka zaya tambayeki, dan haka sai ki tanadi ansar bayarwa tun kafin lokaci ya kure maki.

Shin kinyi abinda ya kamata kiyi ?
Kin rayuwa yanda ya kamata ?

Allah yasa mu dace

©️ Zarah A Zamsarf ✍🏽
Previous Post Next Post