Wani Ba'iraniye ya lashe gasar karatun Kur'ani a Saudiyya

Details from Press TV

Wani Alaramma dan ƙasar Jamhuriyyar Musulunci ta Iran ya zama na farko a musabakar karatun Kur'ani na ƙasa da ƙasa da aka yi a Saudi Arabia.

Malam Younes Shahmoradi shi ne ya zo na daya a musabakar iya karatun Alkur'ani da aka yi, kuma ya samu kyautar Riyal miliyan uku ($800,000) a ranar Juma'a 7 ga Afrilu 2023.

Shahmoradi, wanda yana cikin Alarammomi hudu da suka je zagayen karshe na gasar ya doke Mal. Abdul'aziz al-Faqih dan ƙasar Saudiyya, wanda ya zo na biyu, ya kuma sami kyautar Riyal miliyan biyu ($500,000). 

Sauran 'yan takarar daga Moroko suke, wato Zakariya al-Zirak da Abdullah Al-Dughri, waɗanda suka zo na uku da huɗu bi da bi.

A fagen gasar kiran salla kuwa, 'yan takara daga Saudi Arabia, Indonesia, Lebanon, da Birtaniya ne suka lashe hudun farko.
Previous Post Next Post