YANZU-YANZU: Young Sheikh ya buƙaci Ƙauran Bauchi da ya barshi da Dr. Idris domin kalubantar sa

“Matashin Malamin nan na Addinin Musulunci wato Zakir M.S. Ali Young Sheikh Zariya, Ya Bayyana Cewa; Shine ya fi kamata da ya zauna da Dr. idris Abdulaziz Bauchi saboda sauran malaman sunyi girma akan zama dashi su tattauna mas'alar bayanen taimakon manzon Allah (SAW) idan Musulmi zai yi tawassil da ma'aiki, saɓanin yadda shi Malamin yake ikirarin Musulmi bai kamata ya yi Tawassil da Annabi ba, idan ya ta shi neman wani abu daga wurin Allah (SWA), Matsayar ba Allah ba.”
Dr. Idris Abdul'aziz dai Fitaccen Malamin Addinin Musulunci ne ɗan Asalin jihar Bauchi, ganin yadda kalaman malamanin ya tada ƙura a Najeriya baki daya.”

“Zakir Young Sheikh, ya yi Kira da Babban murya ga gwamnatin jihar Bauchi kan cewa; a hutar da malaman da zasu zauna da shi malamin shi kadai kawai ya ishe shi gayya, zai ta so daga Zariya zuwa Bauchi matsayar na yarje masa.”

Bugu da kari Young. Sheikh ya ce ya tanaji ruwan hujjoji domin gindawa Dr. Idris ɗin a cikin Al-Qur'ani Mai Girma.

Idan dai Allah ya kai mu gobe Asabar ne dai za'ayi wanna zaman da shi Dr. Idris din da wasu malaman Addinin Musulunci, wanda Gwamantin Jihar Bauhci ta ɗauki nauyin wannan Muƙabalan”

Daily True
Previous Post Next Post