Tarihin Rasuwar Ayatullah Ruhollah Musavi Khomeini 1989

Imam Khomeini 

A Rana Mai Kamar Ta Yau 3 Ga Watan Yuni 1989 Wanda Yayi Dai-dai Da 28 Ga Watan Shawwal Shekaru 1409 Bayan Hijra, Allah Ya Karbi Rayuwar Imam Khomeini.

Gwamnatin Sarki Pahlavi ta kama shi har sau biyu kuma ta tilasta masa Yin hijira ta har abada. Ya dade yana zaune a kasar Turkiyya sannan ya koma Birnin Najaf Na Kasar Iraki. 

Ya zauna a Najaf na tsawon shekaru 13 yana koyarwa da rubuce-rubuce da jagorantar masu juyin juya hali a Iran. 

A cikin 1979, an tilasta masa barin Iraki ; don haka ya tafi Birnin Paris na kasar faransa. Bayan wani lokaci ya koma Iran ya jagoranci juyin juya halin Musulunci zuwa ga nasara. Ya kasance jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran har zuwa rasuwarsa a shekara ta 1989.

Musulmi, musamman ‘yan Shi’a, suna girmama shi. Jana'izar sa Ta sami halartar kusan mutane miliyan 10, ita ce jana'izar da ta fi yawan jama'a a duniya har ya zuwa yanzu.

Baya ga ilimin fikihu da ka'idojin fikihu wadanda su ne abubuwan gama gari a makarantun hauza, ya na da ilmin tunani a falsafar Musulunci da sufanci.

Ya Rasu A ranar 28 ga watan Shawwal 1409 daidai Da 3 ga watan Yuni 1989, ya rasu a asibitin zuciya Shahid Raja'i dake Tehran. 

An yi jana'izarsa a ranar 1 ga watan Zul-qa'da 1409 Wanda yazo 5 ga Yuni 1989 a babban Musalla na Tehran. 

Ayatullah Sayyid Muhammad Rida Gulpaygani ya yi sallar jana'izarsa. An binne shi a Bihisht Zahra (wani makabarta a wajen Tehran) a gaban mutane miliyan 10 da suka zo suka zo da kafa daga garuruwa daban-daban na Iran don zaman makoki. 

An tabbatar da jana'izar sa a matsayin jana'izar da aka fi halarta a tarihi.
Previous Post Next Post